Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 17:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra'ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali.

3. Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.

4. Ta karya kan tohonsa mafi tsawo, ta kai shi a ƙasar ciniki, ta dasa shi a birnin 'yan kasuwa.

5. Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi.

6. Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.

7. “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa.

Karanta cikakken babi Ez 17