Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 16:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Sa'ad da na wuce kusa da ke, na gan ki kina birgima cikin jinin haihuwarki, sai na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’ I, na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’

7. Na sa kin girma kamar tsiro a cikin saura. Kika yi girma, kika yi tsayi, kika zama cikakkiyar budurwa, kika yi mama, gashin kanki kuwa ya yi tsawo, amma duk da haka tsirara kike tik a lokacin.

8. “Sa'ad da na sāke wucewa kusa da ke, na dube ki, ga shi, kin kai lokacin da za a ƙaunace ki, sai na yafe miki tufata, na rufe tsiraincinki, na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

9. “Sa'an nan na yi miki wanka da ruwa, na wanke jinin haihuwarki na shafe ki da mai.

10. Na sa miki rigar da aka yi wa ado, na kuma sa miki takalmin fata, na yi miki ɗamara da lilin mai kyau, na yi miki lulluɓi da siliki.

11. Na kuwa caɓa miki ado, na sa mundaye a hannuwanki, da abin wuya a wuyanki.

12. Na kuma sa ƙawanya a hancinki, da 'yan kunne a kunnenki, da kyakkyawan kambi bisa kanki.

13. Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa. Tufafinki kuwa na lilin mai kyau ne, da siliki waɗanda aka yi musu ado. Kin ci lallausan gāri, da zuma, da mai. Kin yi kyau ƙwarai har kin zama sarauniya.

14. Kin shahara a cikin sauran al'umma saboda kyanki, gama kyanki ya zama cikakke saboda ƙawata ki da na yi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. “Amma kin dogara ga kyanki, kika yi karuwanci saboda shahararki. Kin yi ta karuwancinki da kowane mai wucewa.

16. Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa'an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba.

17. Kin kuma ɗauki kayan adonki na zinariyata da azurfata waɗanda na ba ki, kin yi wa kanki siffofin mutane don ki yi karuwanci da su.

Karanta cikakken babi Ez 16