Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 16:53-61 Littafi Mai Tsarki (HAU)

53. Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Zan komo da Saduma da Samariya da 'ya'yansu mata daga bauta. Sa'an nan zan komo da ke daga bauta tare da su,

54. don ki sha ƙasƙanci saboda abin kunyar da kika aikata. Ƙasƙancinki zai ta'azantar da 'yan'uwanki mata.

55. 'Yan'uwanki mata, wato Saduma da 'ya'yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā, Samariya kuma da 'ya'yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā. Ke kuma da 'ya'yanki mata za ku koma kamar yadda kuke a dā.

56. Ashe, ba ƙanwarki, Saduma, ta zama abar karin magana a bakinki a kwanakin fariyarki,

57. kafin asirin muguntarki ya tonu ba? Amma yanzu kin zama abin zargi ga 'ya'yan Edom mata, da waɗanda suke kewaye da ita, da 'ya'yan Filistiyawa mata waɗanda suke kewaye, waɗanda suke raina ki.

58. Kina ɗauke da hukuncin lalatarki da na abubuwanki masu banƙyama, ni Ubangiji na faɗa.”

59. “Ni Ubangiji Allah na ce, zan yi miki yadda kika yi, ke da kika yi rantsuwar kafara, kika ta da alkawari.

60. Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki. Zan ƙulla madawwamin alkawari da ke.

61. Sa'an nan za ki tuna da ayyukanki, ki ji kunya, sa'ad da na ɗauki yarki da ƙanwarki, na ba ki su, su zama 'ya'yanki mata, amma ba a kan alkawarin da na yi da ke ba.

Karanta cikakken babi Ez 16