Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 14:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

13. “Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,

14. ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.

15. “Idan na sa namomin jeji su ratsa cikin ƙasar, su lalatar da ita har ta zama kufai yadda mutum ba zai iya ratsawa ta cikinta ba saboda namomin jejin,

16. ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su ne kaɗai za su tsira, amma ƙasa za ta zama kufai.

17. “Idan kuwa na jawo wa ƙasar takobi, na ce bari takobi ya ratse ƙasar, har na kashe mata mutum duk da dabba,

18. ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su kaɗai za su tsira.

19. Ko kuma na aika da annoba a ƙasar, na kashe mutum duk da dabba da fushina,

20. ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu.

21. “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Balle fa sa'ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba!

22. Idan kuwa waɗansu sun wanzu daga cikinta suka fita da 'ya'yansu mata da maza zuwa wurinta, za ka ga halinsu da ayyukansu, za ka tabbata, masifar da na aukar wa Urushalima, ba kawai ba ne.

23. Bisa ga halinsu da ayyukansu za ka gane abin da na yi musu ba kawai ba ne,’ ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 14