Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 9:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.

11. A ranar ce aka faɗa wa sarki yawan mutanen da aka kashe a Shushan, masarauta.

12. Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”

13. Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai.”

14. Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma.

15. Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.

16. Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba.

17. A rana ta goma sha uku ga watan Adar ne suka aikata wannan abu. A rana ta goma sha huɗu suka huta, suka mai da ranar ta zama ta biki, da farin ciki.

18. Amma Yahudawan da suke a Shushan suka taru a rana ta goma sha uku, da rana ta goma sha huɗu, suka huta ran goma sha biyar, suna biki da murna.

19. Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.

20. Mordekai kuwa ya rubuta abubuwan nan da suka faru, ya aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa waɗanda suke a dukan lardunan sarki Ahasurus, na kusa da na nesa.

21. Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara.

22. Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.

23. Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.

24. Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin dukan Yahudawa, ya ƙulla wa Yahudawa makirci don ya hallaka su. Ya jefa Fur, wato kuri'a don ya hallaka su.

Karanta cikakken babi Esta 9