Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 6:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.

5. Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”Sai sarki ya ce ya shigo.

6. Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”

7. Sai Haman ya ce wa sarki, “Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan.

8. Bari a kawo rigunan sarautar da sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, a kuma sa kambin sarauta a kansa.

Karanta cikakken babi Esta 6