Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 5:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai.

10. Duk da haka Haman ya cije, ya tafi gida. Ya aika a kirawo abokansa da matarsa, Zeresh.

11. Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.

12. Ya ƙara da cewa, “Har ma sarauniya Esta ma ba ta yarda kowa ya tafi tare da sarki wurin liyafar da ta shirya ba, sai ni. Gobe ma ta gayyace ni tare da sarki.

13. Duk da haka wannan bai yi mini daɗi ba, muddin Mordekai, Bayahuden nan, yana zaune a ƙofar sarki.”

14. Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, “Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa'an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa'an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna.”Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen.

Karanta cikakken babi Esta 5