Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 2:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.

2. Sa'an nan barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce masa, “Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa.

3. Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa.

4. Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti.”Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka ɗin.

5. Akwai wani Bayahude a masarauta a Shushan, mai suna Mordekai ɗan Yayir, ɗan Shimai, ɗan Kish mutumin Biliyaminu.

6. An kamo shi a Urushalima tare 'yan zaman talala waɗanda aka kwashe tare da Yekoniya Sarkin Yahuza, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su zaman talala.

7. Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.

Karanta cikakken babi Esta 2