Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 1:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.

5. Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda suke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki.

6. Aka kewaye wurin da fararen labule da na shunayya na lallausan lilin, aka ɗaure da kirtani na lallausan lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa da ginshiƙai na sassaƙaƙƙun duwatsu masu daraja. Akwai gadaje na zinariya da na azurfa a kan daɓen da aka yi da duwatsu masu daraja, masu launi iri iri.

7. Aka ba da sha a finjalai iri iri na zinariya. Aka shayar da su da ruwan inabi irin na sarauta a yalwace bisa ga wadatar sarki.

8. Aka yi ta sha bisa ga doka, ba wanda aka matsa masa, gama sarki ya umarci fādawansa su yi wa kowa yadda yake so.

9. Sarauniya Bashti kuma ta yi wa mata babban biki a fādar sarki Ahasurus.

Karanta cikakken babi Esta 1