Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 9:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta fari ta sarautar Dariyus ɗan Ahazurus Bamediye wanda ya ci sarautar Kaldiyawa,

2. a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.

3. Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.

4. Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba.Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka.

5. “Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.

6. Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa.

Karanta cikakken babi Dan 9