Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 7:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.

5. “Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’

6. “Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.

7. “Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.

8. Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”

9. “Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta,Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa.Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara,Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa,Kursiyinsa harshen wuta ne,Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.

10. Kogin wuta yana gudu daga gabansa.Dubun dubbai suna ta yi masa hidima,Dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa,Aka kafa shari'a, aka buɗe littattafai.

11. “Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone.

12. Sauran dabbobi kuwa aka karɓe mulkinsu, amma aka bar su da rai har wani ƙayyadadden lokaci.

Karanta cikakken babi Dan 7