Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 6:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.

5. Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”

6. Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!

7. Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.

8. Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.”

9. Sai sarki Dariyus ya sa hannu a dokar.

10. Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.

11. Sai mutanen nan suka tafi, suka iske Daniyel yana kai koke-kokensa da roƙonsa ga Allahnsa.

12. Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?”Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”

13. Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”

Karanta cikakken babi Dan 6