Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 5:9-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Belshazzar sarki fa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune, fādawansa duk suka ruɗe.

10. Da sarauniya ta ji maganganun sarki da na manyan fādawansa, sai ta shiga babban ɗakin da ake liyafar, ta ce, “Ran sarki, ya daɗe! Kada ka firgita, kada kuma fuskarka ta turɓune.

11. Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.

12. Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”

13. Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza?

14. Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima.

15. Yanzun nan aka kawo mini masu hikima, da masu dabo don su karanta wannan rubutu, su kuma bayyana mini ma'anarsa, amma sun kāsa faɗar ma'anar rubutun.

16. Amma na ji ka iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya bayyana mini ma'anarsa, to, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin mulkin ƙasar.”

17. Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma'anarsa.

18. “Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.

19. Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.

20. Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

21. Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.

22. “Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.

Karanta cikakken babi Dan 5