Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila.

2. Sa'an nan ya aika a kirawo su hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna, su zo, su halarci bikin keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

3. Sai hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna suka taru don keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Suka kuma tsaya a gaban gunkin.

4. Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta,

5. cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

6. Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.”

7. Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.

8. A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa.

9. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ranka ya daɗe.

10. Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya.

11. Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.

Karanta cikakken babi Dan 3