Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 2:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila.

13. Sai doka ta fita cewa a karkashe masu hikima. Aka nemi Daniyel da abokansa don a kashe su.

14. Daniyel kuwa ya amsa wa Ariyok, shugaban dogaran sarki, a hankali da hikima, sa'ad da Ariyok ya fita don ya karkashe masu hikima na Babila.

15. Daniyel ya ce wa Ariyok shugaban dogaran sarki, “Me ya sa ake gaggauta dokar sarki haka?” Sai Ariyok ya bayyana wa Daniyel yadda al'amarin yake.

16. Sa'an nan Daniyel ya shiga wurin sarki, ya roƙe shi ya ba shi lokaci domin ya yi masa fassarar.

17. Sai Daniyel ya tafi gidansa, ya sanar wa abokansa, wato su Hananiya, da Mishayel, da Azariya da al'amarin.

18. Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.

19. Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.

20. Ya ce,“Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin,Wanda hikima da iko nasa ne.

21. Yana da ikon sāke lokatai,Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu.Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,

22. Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa,Ya san abin da yake cikin duhu.Haske kuma yana zaune tare da shi.

23. A gare ka nake ba da godiya da yabo, ya Allah na kakannina,Gama ka ba ni hikima da iko,Har ka sanar mini da abin da muka roƙe ka,Ka sanar mana da matsalar da ta dami sarki.”

24. Sa'an nan Daniyel ya tafi wurin Ariyok wanda sarki ya sa ya karkashe masu hikima na Babila, ya ce masa, “Kada ka karkashe masu hikima na Babila, ka kai ni gaban sarki, ni kuwa zan yi wa sarki fassarar.”

Karanta cikakken babi Dan 2