Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 2:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Nebukadnezzar ya yi mafarki a shekara ta biyu ta sarautarsa, ya kuwa damu ƙwarai har barci ya gagare shi.

2. Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.

3. Sarki kuwa ya ce musu, “Na yi mafarki, na kuwa matsu ƙwarai in san mafarkin.”

4. Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”

5. Sai sarki ya amsa wa Kaldiyawa, ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini da mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa gunduwa, a mai da gidajenku juji.

6. Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”

7. Suka amsa, suka ce, “Bari sarki ya faɗa wa barorinsa mafarkin, mu kuwa za mu yi maka fassararsa.”

8. Sarki kuwa ya amsa ya ce, “Na sani kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin kun ga na manta da abin.

9. Idan ba ku tuno mini da mafarkin ba, hukuncin kisa ne yake jiranku. Kun haɗa kai don ku yi mini maganganun ƙarya na wofi har lokaci ya wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”

10. Sa'an nan Kaldiyawa suka amsa wa sarki, suka ce, “Ba wani mahaluki a duniya wanda zai iya biyan wannan bukata ta sarki, gama ba wani sarki wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya a wurin mai sihiri, ko mai dabo, ko Bakaldiye.

11. Abin nan da sarki yake so a yi masa yana da wuya, ba wanda zai iya biya wa sarki wannan bukata, sai dai ko alloli waɗanda ba su zama tare da 'yan adam.”

12. Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila.

Karanta cikakken babi Dan 2