Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo Urushalima ya kewaye ta da yaƙi.

2. Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.

3. Sa'an nan Sarkin Babila ya umarci sarkin fādarsa, Ashfenaz, ya zaɓo masa waɗansu samari daga cikin Yahudawa, waɗanda suke daga gidan sarauta, da kuma daga gidan manya,

4. su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa.

5. Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.

Karanta cikakken babi Dan 1