Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 42:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa wa Ubangiji.

2. “Na sani kai kake da ikon yin dukan abu,Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.

3. Wane ne wannan marar ilimi da zai ɓoye shawara?Saboda haka na hurta abin da ban gane ba,Abubuwa waɗanda ban gane ba suna banmamaki ƙwarai.

4. Ka ce, ‘Kasa kunne, zan yi magana da kai,Zan yi maka tambaya, ka ba ni amsa.’

5. Dā jin labarinka nake,Amma yanzu na gan ka ido da ido.

6. Saboda haka na ga ni ba kome ba ne,Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”

7. Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.

Karanta cikakken babi Ayu 42