Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 24:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.

7. Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.

8. Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.

9. “Mugaye sukan bautar da yara marayu,Sukan kama 'ya'ya matalauta a bakin bashin da suke bi.

10. Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.

11. Suna matse mai daga 'ya'yan zaitun.Suna kuma matse ruwan inabi daga 'ya'yan inabi,Amma su kansu suna fama da ƙishi.

12. Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni daWaɗanda suke baƙin mutuwa a birni,Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.

13. “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.

14. Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,Da dare kuma ya yi fashi.

15. Mazinaci yakan jira sai da magariba,Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.

16. Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.

Karanta cikakken babi Ayu 24