Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 24:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sukan saci jakunan marayu,Su kama san gwauruwa,Su ce sai ta biya basusuwanta.

4. Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.

5. Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,Haka matalauta suke,Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.

6. Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.

7. Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.

8. Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.

9. “Mugaye sukan bautar da yara marayu,Sukan kama 'ya'ya matalauta a bakin bashin da suke bi.

10. Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.

Karanta cikakken babi Ayu 24