Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 24:12-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni daWaɗanda suke baƙin mutuwa a birni,Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.

13. “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.

14. Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,Da dare kuma ya yi fashi.

15. Mazinaci yakan jira sai da magariba,Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.

16. Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.

17. Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su,Sun saba da razanar duhu.

18. “Rigyawa takan ci mugun mutum,Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah.Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.

19. Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari,Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.

Karanta cikakken babi Ayu 24