Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 24:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Suna matse mai daga 'ya'yan zaitun.Suna kuma matse ruwan inabi daga 'ya'yan inabi,Amma su kansu suna fama da ƙishi.

12. Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni daWaɗanda suke baƙin mutuwa a birni,Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.

13. “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.

14. Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,Da dare kuma ya yi fashi.

15. Mazinaci yakan jira sai da magariba,Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.

16. Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.

17. Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su,Sun saba da razanar duhu.

18. “Rigyawa takan ci mugun mutum,Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah.Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.

19. Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari,Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.

20. Ba wanda zai tuna da shi,mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba.Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai.Za a sare mugunta kamar itace.

21. Haka yake samun wanda ya wulakanta gwauraye.Bai kuma nuna alheri ga matan da ba su haihu ba.

22. Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi,Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.

Karanta cikakken babi Ayu 24