Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 2:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Mutanen Mowab sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun ƙone ƙasusuwan SarkinEdomDon su yi toka da su.

2. Zan aukar da wuta a ƙasarMowab,Ta ƙone kagarar Keriyot.Jama'ar Mowab za su mutu ahargitsin yaƙi,Sa'ad da sojoji suke sowa, ana busaƙahoni.

3. Zan kashe Sarkin Mowab dashugabannin ƙasar.”

4. Ubangiji ya ce,“Mutanen Yahuza sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun raina koyarwata sun ƙibin umarnaina.Allolinsu na ƙarya waɗandakakanninsu suka bauta wa,Sun sa su su ratse daga hanya.

5. Saboda haka zan aukar da wuta akan YahuzaTa ƙone kagarar Urushalima.”

6. Ubangiji ya ce,“Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun sayar da salihai waɗandasuka kāsa biyan bashinsu.Sun kuma sayar da matalautaWaɗanda bashinsu bai kai ko kuɗinbi-shanu ba.

Karanta cikakken babi Amos 2