Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 9:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.

2. Sulemanu kuwa ya amsa dukan tambayoyin da ta yi masa, ba wani abu da yake ɓoye ga Sulemanu wanda ya kāsa bayyana mata.

3. Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina,

4. da irin abincin da yake kan tebur ɗinsa da irin zaman manyan mutanensa, da barorin da yake yi masa hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da irin tufafinsu, ta kuma ga hadayun ƙonawa da yake miƙawa a Haikalin Ubangiji, sai ta ji ba ta da sauran kuzari.

5. Sarauniya ta ce wa sarkin, “Ashe, gaskiya ce, labarinka da na ji a ƙasata a kan al'amuranka da hikimarka.

6. Amma dā ban gaskata labarinsu ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabin yawan hikimarka ma ba a faɗa mini ba. Ashe, duk labarin da aka faɗa mini, ka zarce haka ƙwarai.

7. Masu farin ciki ne mutanenka, da barorinka waɗanda suke yi maka hidima kullayaumin, gama kullum suna jin hikimarka.

Karanta cikakken babi 2 Tar 9