Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 36:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.

6. Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila.

7. Nebukadnezzar kuma ya kwaso waɗansu tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya kai Babila, ya ajiye su a fādar Babila.

8. Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.

9. Yekoniya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

10. Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.

11. Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.

12. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.

13. Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila.

14. Dukan manyan firistoci da sauran jama'a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al'ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Tar 36