Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 36:20-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na 'ya'yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,

21. don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba'in, ta kiyaye asabatai.

22. Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

23. Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”

Karanta cikakken babi 2 Tar 36