Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 35:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa 'yan'uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”

7. Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da 'yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne.

8. Da yardar rai manyan ma'aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama'ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma'aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku.

9. Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, 'yan'uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da 'yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.

10. Sa'ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta.

11. Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa'an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa.

12. Sa'an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Haka nan kuma suka yi da bijiman.

Karanta cikakken babi 2 Tar 35