Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 32:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.

8. Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.

9. Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,

10. “Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, ‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta?

11. Ai, Hezekiya, ba ruɗinku yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi sa'ad da yake ce muku Ubangiji Allahnku zai cece ku daga hannun Sarkin Assuriya?

12. Ashe, ba wannan Hezekiya ba ne ya ɗauke masujadansa da bagadansa, ya kuma umarci Yahuza da Urushalima, su yi sujada a gaban bagade guda, a kansa ne kuma za su ƙona hadayu?

13. Ashe, ba ku san abin da ni da kakannina muka yi wa dukan jama'ar waɗansu ƙasashe ba? Gumakan al'umman waɗannan ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna?

Karanta cikakken babi 2 Tar 32