Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 29:7-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila.

8. Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba'a kamar yadda kuke gani da idanunku.

9. Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, 'ya'yanmu mata, da 'ya'yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.

10. “Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.

11. 'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”

12-14. Sa'an nan sai Lawiyawa suka tashi,na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya,na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel,na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa,na Elizafan, Shimri da Yehiyel,na Asaf, Zakariya da Mattaniya,na Heman, Yehiyel da Shimai,na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.

15. Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji.

16. Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.

17. A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.

18. Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki.

19. Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa'ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”

20. Sarki Hezekiya kuwa ya tashi da sassafe ya tattara manyan gari suka haura zuwa Haikalin Ubangiji.

21. Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da 'yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato 'ya'yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji.

22. Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka nan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.

23. Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran.

24. Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra'ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra'ila.

25. Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.

26. Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni.

Karanta cikakken babi 2 Tar 29