Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.