Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 26:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan jama'ar Yahuza fa suka ɗauki Azariya, ɗan shekara goma sha shida, suka naɗa shi sarki, ya gāji gadon sarautar tsohonsa Amaziya.

2. Ya gina Elat, ya komar da ita ga Yahuza, bayan rasuwar sarki.

3. Azariya yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu, sunan tsohuwarsa Yekoliya ta Urushalima.

4. Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata.

5. Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.

6. Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 26