Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 24:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra'ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.

17. Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya'a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa.

18. Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.

19. Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.

20. Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama'a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”

21. Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.

22. Sarki Yowash bai tuna da irin alherin da Yehoyada mahaifin Zakariya ya yi masa ba, amma ya kashe ɗansa. Sa'ad da Zakariya yake bakin mutuwa, sai ya ce, “Bari Ubangiji ya gani ya kuma sāka.”

23. A ƙarshen shekara sai sojojin Suriyawa suka kawo wa Yowash yaƙi suka je Yahuza da Urushalima, suka hallaka dukan shugabannin jama'a, suka kwashi ganima mai yawa, suka aika wa Sarkin Dimashƙu.

24. Ko da yake mutanen Suriya kima ne, duk da haka Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan babbar rundunar Yowash, saboda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu. Ta haka suka hukunta wa Yowash.

Karanta cikakken babi 2 Tar 24