Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 23:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama'a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!”

14. Sai Yehoyada, firist, ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku kawo ta a tsakiyar sojoji, duk wanda ya bi ta a kashe shi da takobi.” Gama firist ɗin ya ce, “kada ku kashe ta a Haikalin Ubangiji.”

15. Sai suka kama ta. Da suka kai Ƙofar Doki ta fādar sarki, sai suka kashe ta a can.

16. Sai Yehoyada da dukan jama'a, da sarkin, suka ɗauki alkawari za su zama jama'ar Ubangiji.

17. Sai dukan jama'a suka tafi gidan Ba'al, suka rushe shi, suka kuma ragargaza bagadansa, da siffofinsa. Suka kashe Mattan, firist ɗin Ba'al, a gaban bagadan.

18. Yehoyada kuma ya sa matsaran da za su yi tsaron Haikalin Ubangiji a ƙarƙashin ikon firistoci, Lawiyawa, waɗanda Dawuda ya shirya don su lura da Haikalin Ubangiji, su miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, yadda aka rubuta a Attaura ta Musa, da murna da waƙa kamar yadda Dawuda ya shirya.

19. Ya kuma sa 'yan tsaron ƙofa a ƙofofin Haikalin Ubangiji, don kada wani marar tsarki na kowane iri ya shiga.

20. Sai ya sa shugabanni, da dattawa, da masu mulki, da dukan jama'ar ƙasar, suka rufa wa sarki baya, daga Haikalin Ubangiji suka bi ta Ƙofar Bisa zuwa fādar sarki. Suka zo suka zaunar da sarki a gadon sarauta.

21. Dukan jama'ar ƙasar suka yi murna, zaman lafiya ya komo birnin, bayan da an kashe Ataliya.

Karanta cikakken babi 2 Tar 23