Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 21:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Har wa yau Edom ya tayar wa Yahuza. A wannan lokaci kuma Libna ta tayar wa mulkinsa, saboda Yoram ya rabu da bin Ubangiji Allah na kakanninsa.

11. A kan wannan kuma, ya yi masujadai a tuddan ƙasar Yahuza, ya sa mutanen Urushalima su zama marasa aminci, ya sa Yahuza ta ratse.

12. Sai annabi Iliya ya rubuta masa wasiƙa ya ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na tsohonka Dawuda ya ce, ‘Da yake ba ka bi halin tsohonka Yehoshafat ba, da halin Asa Sarkin Yahuza,

13. amma ka bi irin halin sarakunan Isra'ila, har ka sa Yahuza da mazaunan Urushalima su zama marasa aminci, yadda gidan Ahab ya yi, ka kuma karkashe 'yan'uwanka, waɗanda kuke uba ɗaya, waɗanda suka fi ka kirki,

14. ga shi, ni Ubangiji zan aukar da babbar abboba a kan jama'arka, da 'ya'yanka maza, da matanka, da a kan abin da ka mallaka duka.

15. Kai da kanka kuma za ka kamu da ciwon hanji mai tsanani, saboda tsananin ciwo, hanjinka zai tsintsinke ya yi ta zuba kowace rana.’ ”

16. Sai Ubangiji ya kuta Filistiyawa da Larabawan da suke kusa da Habashawa, su yi gāba da Yoram.

17. Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe 'ya'yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 21