Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 15:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra'ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa'ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.

10. Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa.

11. A ran nan suka miƙa wa Ubangiji hadayun bijimai ɗari bakwai, da tumaki dubu bakwai (7,000) daga cikin ganimar da suka kwaso.

12. Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu.

13. Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra'ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji.

14. Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho.

15. Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al'amari.

16. Asa kuma ya tuɓe tsohuwarsa, Ma'aka, daga matsayinta na sarauniya don ta ƙera wata siffa mai banƙyama ta Ashtoret. Sai Asa ya sare siffar nan, ya niƙe ta, ya ƙone a rafin Kidron.

Karanta cikakken babi 2 Tar 15