Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 1:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya.

10. Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”

11. Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama'ata wadda na naɗa ka sarki a kanta,

12. to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”

13. Daga nan sai Sulemanu ya taso daga masujadar da take Gibeyon inda alfarwa ta sujada take, ya zo Urushalima inda ya zauna yana mulkin Isra'ila.

14. Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi.

15. Sarki ya yawaita azurfa da zinariya har suka zama kamar duwatsu a Urushalima. Haka kuma ya yi da itatuwan al'ul, suka yawaita kamar itatuwan ɓaure a fadama.

16. Wakilan sarki suka ɗauki nauyin shigo da dawakai daga Masar da Kilikiya,

17. suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.

Karanta cikakken babi 2 Tar 1