Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 5:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra'ila da takarda.”Na'aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya.

6. Ya kai wa Sarkin Isra'ila tarkardar, wadda ta ce, “Sa'ad da wannan takarda ta sadu da kai, ka sani fa, ni ne na aiko barana, Na'aman, wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa.”

7. Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”

8. Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”

9. Na'aman kuwa da dawakansa da karusansa suka tafi suka tsaya a ƙofar gidan Elisha.

10. Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na'aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka.

11. Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.

Karanta cikakken babi 2 Sar 5