Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 3:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Yehoshafat kuwa ya ce, “Gaskiya ne, maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sai sarakunan nan uku suka ɗunguma zuwa wurin Elisha.

13. Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.”Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”

14. Elisha ya amsa ya ce, “Na rantse da Ubangiji Mai Runduna, wanda nake bautarsa, da ba domin ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuza ba, da ba zan kula da kai har ma in dube ka ba.

15. Amma yanzu ku kawo mini makaɗin garaya.”Da makaɗin garaya ya kaɗa, sai ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha.

16. Sai ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ku haƙa kududdufai a kwarin nan.

17. Ko da yake ba ku ga iska, ko ruwan sama ba, duk da haka kwarin zai cika da ruwa domin ku sha, ku da dabbobinku.’

18. Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji, zai kuma ba da Mowabawa a hannunku.

19. Za ku ci kowane birni mai garu da kowane birni na musamman. Za ku sassare kowane kyakkyawan itace, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku lalatar da gonaki masu kyau da duwatsu.”

20. Kashegari, da safe a lokacin miƙa hadaya, sai ga ruwa ya malalo daga wajen Edom har ƙasar ta cika da ruwa.

21. Da Mowabawa suka ji labari, sarakuna sun kawo musu yaƙi, sai dukan waɗanda suka isa ɗaukar makamai, daga ƙarami zuwa babba, aka kirawo su, suka ja dāga a kan iyaka.

22. Sa'ad da suka tashi da sassafe, rana tana haskaka ruwa, sai suka ga ruwan a gabansu ja wur kamar jini.

23. Sai suka ce, “Wannan jini ne, hakika sarakunan sun yi yaƙi da juna, sun karkashe juna. Bari mu tafi mu kwashi ganima!”

Karanta cikakken babi 2 Sar 3