Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 3:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.

2. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, amma bai kai na tsohonsa da tsohuwarsa ba, gama ya kawar da ginshiƙin gunkin nan Ba'al wanda tsohonsa ya yi.

3. Duk da haka, bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.

4. Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra'ila 'yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara.

5. Amma da Ahab ya rasu, Sarkin Mowab kuwa ya tayar wa Sarkin Isra'ila.

6. Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra'ila duka.

7. Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?”Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka.

8. Wace hanya za mu bi?”Yehoram kuwa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 3