Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 25:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.

18. Nebuzaradan kuma ya tafi da Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofa.

19. Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da 'yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama'ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin.

20. Nebuzaradan shugaban sojoji ya kai su wurin Sarkin Babila a Ribla ta ƙasar Hamat.

21. Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can.Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.

22. A kan sauran waɗanda suka ragu a ƙasar Yahuza, waɗanda Sarkin Babila, Nebukadnezzar, ya bari, ya naɗa musu Gedaliya ɗan Ahikam, wato jikan Shafan, ya zama hakiminsu.

23. Sa'ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma'aka.

24. Sai Gedaliya ya rantse musu, su da mutanensu, cewa kada su ji tsoron barorin Kaldiyawa, su zauna a ƙasar, su bauta wa Sarkin Babila, haka zai fi zamar musu alheri.

25. Amma a watan bakwai, sai Isma'ilu ɗan Netaniya, wato jikan Elishama, daga gidan sarauta, ya zo tare da mutum goma ya fāda wa Gedaliya, ya kashe shi tare da Yahudawa da Kaldiyawa da suke tare da shi a Mizfa.

26. Sai dukan mutane, manya da ƙanana, da shugabannin mayaƙa, suka tashi, suka gudu zuwa Masar, gama sun ji tsoron Kaldiyawa.

27. A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar.

28. Ya yi masa magana mai kyau, ya kuma ba shi matsayi fiye da sarakunan da suke tare da shi a Babila.

Karanta cikakken babi 2 Sar 25