Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 25:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.

13. Sai Kaldiyawa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalansu, da kwatarniyar ruwa na tagullar da take cikin Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagullar zuwa Babila.

14. Suka kuma kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da cokula, da tasoshin tagulla da ake amfani da su don hidimar Haikali.

15. Suka kuma kwashe farantan wuta da daruna. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban sojojin ya kwashe.

16. Tagullar da Sulemanu ya yi abubuwan nan da su, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.

17. Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.

18. Nebuzaradan kuma ya tafi da Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofa.

19. Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da 'yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama'ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin.

20. Nebuzaradan shugaban sojoji ya kai su wurin Sarkin Babila a Ribla ta ƙasar Hamat.

21. Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can.Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.

22. A kan sauran waɗanda suka ragu a ƙasar Yahuza, waɗanda Sarkin Babila, Nebukadnezzar, ya bari, ya naɗa musu Gedaliya ɗan Ahikam, wato jikan Shafan, ya zama hakiminsu.

Karanta cikakken babi 2 Sar 25