Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 24:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A zamanin Yehoyakim ne Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo wa Yahuza yaƙi, Yehoyakim kuwa ya zama baransa har shekara uku daga nan kuma ya tayar masa.

2. Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa.

3. Hakika haka ya faru ga Yahuza bisa ga umarnin Ubangiji domin a kawar da su daga gaban Ubangiji saboda dukan zunubin Manassa da ya aikata,

4. saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.

5. Sauran ayyukan Yehoyakim da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

6. Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.

7. Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.

8. Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Sar 24