Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 23:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da 'yan'uwansu.

10. Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin 'ya'yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek.

11. Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana.

12. Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron.

13. Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.

14. Ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffofin gumakan, sa'an nan ya rufe wurarensu da ƙasusuwan mutane.

15. Yosiya ya kuma rushe bagaden da yake a Betel, wanda Yerobowam ɗan Nebat ya gina, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi, tare da tudun, ya farfashe duwatsun, ya niƙe su, sun zama gari, ya kuma ƙone Ashtoret.

16. Da Yosiya ya waiwaya, sai ya ga kaburbura a kan dutse. Ya aika a kwaso ƙasusuwan da suke cikin kaburburan, sai ya ƙone su a bisa bagaden, ya lalatar da shi kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi.

17. Ya kuma ce, “Kabarin wane ne wancan da nake gani?”Sai mutanen Betel suka ce masa, “Ai,kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuza ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”

18. Sarki kuwa ya ce, “A bar shi yadda yake, kada wani ya taɓa ƙasusuwansa.”Sai suka bar ƙasusuwan annabin da ya zo daga Samariya.

19. Dukan matsafai na kan tuddai da suke a garuruwan Samariya waɗanda sarakunan Isra'ila suka gina, har suka sa Ubangiji ya yi fushi, Yosiya ya watsar da su. Ya yi da su kamar yadda ya yi a Betel.

20. Ya kuma karkashe dukan firistocin matsafai na kan tuddai a bisa bagadan da suke can. Ya ƙone ƙasusuwansu a bisa bagadan. Sa'an nan ya komo Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Sar 23