Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:28-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”

29. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu.

30. Ringin mutanen gidan Yahuza za su yi saiwa a ƙasa, sa'an nan su ba da 'ya'ya a sama.

31. Gama daga Urushalima ringi zai fito, daga Dutsen Sihiyona kuma waɗanda suka tsira za su fito. Kishin Ubangiji ne zai yi wannan.”

32. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Sarkin Assuriya ba zai zo birnin ba, ko ya harba kibiya, ko ya zo kusa da shi da garkuwa, ko ya tsiba masa tudu.

33. Zai koma ta hanyar da ya zo. Ba zai shiga wannan birni ba.

34. Gama zan tsare wannan birni, in cece shi don kaina, da kuma don bawana Dawuda.”

35. A daren nan, sai mala'ikan Ubangiji ya tafi ya kashe Assuriyawa a sansaninsu, mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Sa'ad da mutanen Isra'ila suka tashi da sassafe, sai suka ga gawawwakin nan kwance.

36. Sennakerib Sarkin Assuriya, kuwa ya tashi, ya koma gida, ya zauna a Nineba.

37. Sa'ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19