Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ka yi fariya a kan gina rijiyoyi, ka sha ruwan baƙuwar ƙasa, ƙafafun sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu, ya ƙafe.

25. “Ba ka taɓa ji ba, cewa na ƙaddara wannan tun dā? Abin da yake faruwa yanzu, na shirya shi tun tuni, yadda za ka mai da birane masu garu su zama kufai.

26. Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.

27. “Na san zamanka, da fitarka, da shigowarka, da fushin da kake yi da ni.

28. Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”

29. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu.

30. Ringin mutanen gidan Yahuza za su yi saiwa a ƙasa, sa'an nan su ba da 'ya'ya a sama.

31. Gama daga Urushalima ringi zai fito, daga Dutsen Sihiyona kuma waɗanda suka tsira za su fito. Kishin Ubangiji ne zai yi wannan.”

32. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Sarkin Assuriya ba zai zo birnin ba, ko ya harba kibiya, ko ya zo kusa da shi da garkuwa, ko ya tsiba masa tudu.

33. Zai koma ta hanyar da ya zo. Ba zai shiga wannan birni ba.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19