Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 18:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar.

2. Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abi, 'yar Zakariya.

3. Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

4. Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.

5. Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.

6. Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.

7. Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa.

8. Ya kuma bugi Filistiyawa har zuwa Gaza da iyakarta daga hasumiya zuwa birni mai garu.

9. A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra'ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta.

10. A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta.

11. Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.

12. Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.

13. A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.

Karanta cikakken babi 2 Sar 18