Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 17:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na 'yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba'al.

17. Suka yi hadaya ta ƙonawa da 'ya'yansu mata da maza. Suka yi duba, suka yi sihiri, suka duƙufa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji, suka sa shi ya yi fushi.

18. Saboda wannan Ubangiji ya husata da jama'ar Isra'ila, ya kawar da su daga gabansa, ba wanda aka rage, sai dai kabilar Yahuza.

19. Jama'ar Yahuza kuma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba, sai suka bi al'adun da mutanen Isra'ila suka kawo.

20. Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra'ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa.

21. Sa'ad da Ubangiji ya ɓalle Isra'ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama'ar Isra'ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi.

22. Jama'ar Isra'ila suka yi ta aikata dukan zunuban da Yerobowam ya yi, ba su daina aikata su ba.

23. har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama'ar Isra'ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau.

24. Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama'ar Isra'ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta.

Karanta cikakken babi 2 Sar 17