Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 13:7-16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.

8. Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

9. Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.

10. A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta.

11. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat.

12. Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfin da ya yi yaƙi da Amaziya Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.2Sar 14.15; 1Sar 15.31

13. Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra'ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.

14. Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”

15. Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka.

16-17. Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 13