Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 10:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba'al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa.

19. Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.

20. Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron,

21. sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.

22. Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.

23. Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba'al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba'al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba'al sujada kaɗai.”

24. Sa'an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”

25. Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa'an nan suka shiga can cikin haikalin Ba'al.

26. Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.

27. Suka yi kaca kaca da gunkin Ba'al da haikalinsa, suka mai da haikalin ya zama salga har wa yau.

28. Yehu ya kawar da Ba'al daga cikin Isra'ila.

29. Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.

Karanta cikakken babi 2 Sar 10