Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 1:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba, na uku ke nan, tare da mutanensa hamsin. Sai shugaba na uku ya tafi ya rusuna a gaban Iliya, ya roƙe shi, ya ce, “Ya mutumin Allah, ina roƙonka ka ga darajar raina da na barorinka, su hamsin.

14. Gama wuta ta sauko daga sama ta cinye shugabanni biyu tare da mutanensu hamsin hamsin, amma ka dubi darajar raina.”

15. Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Ka sauka, ka tafi tare da shi, kada ka ji tsoronsa.” Iliya kuwa ya tashi, ya tafi tare da shi har gaban sarki.

16. Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba'alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra'ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.’ ”

17. Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.

18. Sauran ayyukan da Ahaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

Karanta cikakken babi 2 Sar 1